Muhammed Bello (Larabci: محمد بلو) Shi ne sarki Sarkin Musulmi na biyu. Ya yi mulki daga shekara ta 1817 har zuwa shekara ta 1837. Ya kasance marubucin tarihi ne wanda ke da Ilimin addinin Musulunci. Ɗan Usman dan Fodio ne kuma mai masa hidima, wanda shi ne ya kafa Daular Sokoto kuma shi ne Sultan (Sarkin Musulmi) na farko. Lokacin mulkinsa, ya ƙarfafa da'awar yada Musulunci a dukkanin yankunan Kasar Hausa, da tsarin karantar da mata da maza, da kuma kafa kotunan Musulunci, Ya rasu a watan Octobar 25, shekarar 1837, kaninsa Abu Bakar Atiku ne ya gaje shi, daga nan sai dansa mai suna Ali Babba bin Bello ya gaji sarautar a gurin Abubakar Atiku.
Yau 27 ga watan Yuli na 2022
Ga wasu muhimman abubuwa na tarihi da suka faru a wannan rana.
1996 - A rana irin ta yau a shekara ta 1996 wani bututun mai ya fashe a filin shakatawa na Olympic Centennial da ke birnin Atlanta na kasar Georgia, inda ya kashe mutum 1 tare da raunata mutane 111 a harin ta'addanci na farko da aka yi a gasar Olympics tun bayan gasar 1972 a birnin Munich na Yammacin Jamus.
1953 - An rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da makamai da za ta kawo karshen yakin Koriya a P'anmunjŏm da ke tsakiyar Koriya.
1919 - Rikici ya ɓalle a Chicago bayan da aka sace tare da ɓatar da wani matashi Bakar fata kuma aka nutsar da shi a tafkin Michigan saboda yin iyo a wani yanki da aka kebe don farar fata kaɗai
1214 - A yakin Bouvines, Sarkin Faransa Philip II ya yi nasara a kan kawancen kasa da kasa karkashin jagorancin Sarkin Roma mai tsarki Otto IV.
2012 - Sarauniya Elizabeth ta biyu a hukumance ta bude gasar Olympics ta lokacin bazara ta 2012 a London
Wannan dai shi ne karo na 3 da birnin Landan ke karɓar baƙuncin gasar wasanni ta ƙasa da ƙasa da dama. An kira bikin ne Isles of Wonder kuma Danny Boyle ne ya ba da umarni
1985 - juyin mulki a Uganda Tito Lutwa Okello, wani hafsan sojan Uganda ya yi nasarar yin juyin mulki kan shugaba Milton Obote. Shugaban kasar mai ci Yoweri Museveni ya hambarar da shi bayan watanni 6.
Kwale kwale mafi tsufa da aka taɓa ganowa a nahiyar Afrika, kuma na uku mafi tsufa a duniya shine wanda wani bafulatani ya gano a shekara ta 1987 a ƙyauyan Dunfuna dake ƙaramar hukumar Fume dake jihar Yobe.
A shekara ta 1967, shugaban Najeriya Yakubu Gowon ya raba shiyoyin Najeriya zuwa Jihohi goma sha biyu.
Ƙasar Thailand itace kawai ƙasar da turawa basu yiwa mulkin mallaka ba a yankin kudu maso gabashin Asiya.
Mutanen ƙasar Holand sune suka fi tsawo a duniya.
Ƙasar Brazil itace tafi samar da lemu a duniya.
Tsohon shugaban Najeriya Janaral Murtala Mohammed shine ya kafa tubalin gina babban birnin Tarayyar Najeriya wato Abuja saboda babban birnin Nigeria a wancan lokacin wato Lagos yana fama da cunkoson jama'a. Ya zaɓi tawagar mutane bisa jagorancin mai shari'a Akinola Aguda wanda ya zaɓi Abuja a matsayin sabon gurin da za'a gina babban birnin Nigeria
Kashi ishirin da uku ne kawai na mutanen ƙasar New Zealand suke haihuwar sama da 'ya 'ya biyu.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ajax ta kori kocinta Alfred Schreuder bayan gaza cin ko wasa ɗaya cikin bakwai da ya jagoranci ƙungiyar.
A Najeriya al'ummar ƙasar na cikin wani irin yanayi a yayin da wa'adin da gwamnatin ƙasar ta tanadar na dena amsar tsofaffin takardun kuɗin ƙasar na ₦200, ₦500, ₦1000
A Jihar Osun dake kudancin Nigeria, Kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ta ayyana Oyetola a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan wanda aka gudanar a bara. Alƙalin kotun Mai Shari'a Tertsea Kume ita ta tabbatar da cewa tsohon gwamman ne ya ci zaɓen.
Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai na jam'iyyar PDP a mazaɓar Birnin Kebbi da Kalgo da Bunza da e Jihar Kebbi, Abba Muhammed Bello, ya rasu.