Misra
Misra | |||||
---|---|---|---|---|---|
جُمهورِيّةُ مِصرَ العَرَبيّةِ (ar) | |||||
|
|||||
| |||||
Take | Bilady, Bilady, Bilady (en) | ||||
| |||||
| |||||
Suna saboda | Ptah (en) da Mizraim (en) | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Babban birni | Kairo, Thinis (en) da Memphis, Egypt | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 94,798,827 (2017) | ||||
• Yawan mutane | 93.82 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Larabci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na | Arewacin Afirka, Gabas ta tsakiya da Yammacin Asiya | ||||
Yawan fili | 1,010,407.87 km² | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Mediterranean Sea (en) da Nil | ||||
Wuri mafi tsayi | Mount Catherine (en) (2,629 m) | ||||
Wuri mafi ƙasa | Qattara Depression (en) (−133 m) | ||||
Sun raba iyaka da |
| ||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Kingdom of Egypt (en) da All-Palestine Government (en) | ||||
Ƙirƙira |
28 ga Faburairu, 1922: Kingdom of Egypt (en) 3150 "BCE" | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Tsarin gwamnati | jamhuriya | ||||
Gangar majalisa | Parliament of Egypt (en) | ||||
• President of Egypt (en) | Abdul Fatah el-Sisi (8 ga Yuni, 2014) | ||||
• Prime Minister of Egypt (en) | Moustafa Madbouly (en) | ||||
Ikonomi | |||||
Kuɗi | Egyptian pound (en) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Suna ta yanar gizo | .eg (en) da .مصر (en) | ||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +20 | ||||
Lambar taimakon gaggawa | 122 (en) , 123 (en) da 180 (en) | ||||
Lambar ƙasa | EG | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | egypt.travel |
Kasar Misra ko Masar tana ɗaya daga cikin muhimman siffofin da take taƙama da su shi ne na kasancewarta a kan mararraba.ta kusa da nahiyar Turai, sannan kuma tana matsayin ƙasar da ta kasance mashiga tsakanin Afirka da nahiyar Asiya. Har ila yau kuma, ita ce ta haɗa hanyar safara ta cikin ruwa, tsakanin tekun Mediterrenean da tekun Indiya ta hanyar bahar Maliya.
Dalar Giza da ke birnin Al-ƙahirar Kasar. Misra ko kasar Masar dai ta kasance ƙasa mafi yawan al'umma a cikin dukkanin ƙasashen Larabawa, kuma babban birninta wato birnin Al'ƙahira shi ne birni mafi girma a nahiyar Afirkatun ƙarnoni da dama da suka gabata. Sannan kuma har ila yau ga ta a ƙarshen kogin nilu, wanda shi ne kogi mafi girma a duniya. Saboda haka idan aka yi la'akari da waɗannan dalilai na tarihi, to za a iya fahimtar dalilin da ya sa matsayin ƙasar Misra yake da 'yar rikitarwa.
Suma kansu Misirawan a tsakanin su, sukan kasance cikin ruɗani a game da batun nahiyar da ya kamata su yi tutiya da ita a matsayin nahiyarsu. Ga su dai a cikin kwazazzabon nilu, da mediterenean, da Sahara, har ila yau kuma ga su cikin duniyar Musulmai, duk kan waɗannan siffofi, siffofi ne da ba kasafai ya kamata a ce wata ƙasa guda ɗaya ta haɗa su ba. To sai dai duk da haka za a iya cewa, mafi yawan faɗin ƙasar yana ɓangaren nahiyar Afirka ne. To amma fa duk da haka ana kallon garuruwan da suke lardin sinai na ƙasar Misiran a matsayin ɓangaren nahiyar Asiya, kasancewar su, suna yankin gabashin ƙasar ne.
Kogin Nilu wanda shi ne kogi mafi girma a duniya. A zamanin da can, dangantakar Misra da ƙasashen da ke Afirka na da matukar ƙarfi. To amma tun lokacin da Siriyawa da ke ƙarƙashin daular Rumawa suka mamaye Misira, a ƙarni na bakwai kafin zuwan Annabi Isa Alaihissalam, sai Misira ta fuskanta zuwa ga Yankin Gabas ta Tsakiya, ta fuskar harkokin al'adunta da na addininta da na siyasarta da kuma na tattalin arzikinta. Kuma mafiya yawan Misirawa suna danganta kansu ne da Larabawa kuma 'yan Yankin Gabas ta Tsakiya. Har ila yau kuma wasu dayawa daga cikinsu, kusan ace waɗanda suke su ne 'yan asalin ƙasar ta Misira, waɗanda kuma akafi sani da Nubiyawa, suna danganta kansu ne da Afirka. Hasalima suna iƙirarin su jinin Afirka ne.
Babu shakka dai idan aka bi salsala ta tarihi, shekaru 200 da suka gabata, Misra tana da alaƙa mai ƙarfi da ƙasashe irin su Sudan da Habasha da Libya da ma wasu ƙasashe da dama na nahiyar ta Afirka. Kuma ba tare da wani kokwanto ba, Misra za ta ci gaba da cin tudu biyu, a matsayinta na ruwa-biyu, wato ga ta dai 'yar Afirka, kuma 'yar yankin Gabas ta Tsakiya,yana daga cikin tarihi misra itace gari na farko a tarihi da shedan da kansa ya bayyana ga azzalumin sarki fir auna a lokacin da fir auna yace shine ubangiji.
Tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]
Kasan tana da matukar tarihin gaske a yankin Afirka da duniya gabaki daya
Al'adu[gyara sashe | Gyara masomin]
Abinci[gyara sashe | Gyara masomin]
Tufafi[gyara sashe | Gyara masomin]
Yarika[gyara sashe | Gyara masomin]
Mulki[gyara sashe | Gyara masomin]
Kasan misra tana da karfin mulki.
Arziki[gyara sashe | Gyara masomin]
Noma[gyara sashe | Gyara masomin]
Kasan misra suna da dabino da fure daban daban.
Kiwon lafiya[gyara sashe | Gyara masomin]
Akwai asibitoci da'ake kula da marasa lapiya
Wasanni[gyara sashe | Gyara masomin]
Addini[gyara sashe | Gyara masomin]
Musulunci[gyara sashe | Gyara masomin]
Kiristanci[gyara sashe | Gyara masomin]
Tsaro[gyara sashe | Gyara masomin]
Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]
Ƙasashen Afirka |
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe |