Tattalin arziki

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Wikidata.svgtattalin arziki
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na social system (en) Fassara
Karatun ta ikonomi, economic anthropology (en) Fassara da Mai tattala arziki
wani yanayi na bunkasa tattalin arziki a yayin kullen Korona virus

Tattalin Arziki (Economy) ya dogara ne akan samar da abinci, sutura, ayyuka, kiwon lafiya, Ilimi, Gine-gine da sauransu, da kuma rarrabasu, da cinikayyarsu har zuwa ga amfani dasu ga al'umma. Tattalin arziki shine bunkasawa, aiwatarwa da habaka ayyukan dake kawo cigaban kasa, ta hanyar dogara akan fitar da amfani daga ayyukan da mutum keyi dan anfanar kansa da kuma kula dasu. Abubuwan dake habaka tattalin arzikin kasa sune, mutane, kasuwanci, Ma'aikatu, da gwamnati. Ayyukan tattalin arziki yafara ne tun daga cinikayya, wato a sanda mutane biyu suka kulla yarjejeniyar cimma ciniki akan wani abu da akeso, ta hanyar amfani da kudi ko wani abu maidaraja kamar zinari,azurfa, tagulla da dai sauransu,duk da yake ana ganin cinikayya ta kudi kawai wani karamin abune idan ana magana akan tattalin arzikin kasa.

Tattali arziki na samun zimma ne tun daga samar da ayyuka ko abubuwan dake amfani da albarkatun kasa ko ma'adinai, aikin dan'adam, da sa jari. Amma haka ya canja sanadiyar canjin rayuwa, da kuma cigaban fasahar dan'adam wurin amfani da injina masu sarrafa Kansu, yakawo samun sauki da saurin aikata ayyuka,da kuma rage kudin da ayyukan kansa, Haka nan kuma samun cigaba wurin kirkiran sabbin abubuwa, sabbin hanyoyin aiki, sabbin hanyoyin gabatar da ayyuka, manya manya kasuwanni, kasuwannin dasuka tattari abubuwa daban-daban, an kuma sami karin kudinshiga.

Tattalin arziki yana samun nasara ne sanadiyar ayyukan al'adun al'ummah, martabarsu, iliminsu, fadadar fasaharsu, Tarihinsu, tsarin al'ummarsu, tsarin tafiyar da siyasarsu da dokokinsu, har wayau da kuma irin yanayin kasar, ma'adinan kasa, da yanayin rayuwar halittun kasar, wadannan sune ke bayar da cikkakiyar samun habakar arzikin kasa, kuma wadannan abubuwan suke bada guri da abubuwan da arziki ke cigaba dasu sannan ya tsarasu akan anfanuwar kasa da al'umman ta.

Akwai tattalin arziki daya dogara kacokan akan kasuwanci, kuma yana gudana ne akan cinikayyar ayyuka ko kayayyaki tsakanin mutane, ta hanyar samar dasu da kaisu kasuwanni domin cinikinsu da kudade ko dai wani abunda aka kayyade mai daraja.

Akwai tattalin arziki daya dogara akan bayar da umurni daga 'yan'siyasa kaitsaye da kula da yadda ake samar wa 'yankasa da ayyuka ko kayayyaki da kuma yadda za'a saidar dasu da rarraba su.

Akwai tattalin arziki daya dogara akan ma'adinan kasa, da sanya al'umma acikin gudanarwar su..